Jirgui blood and beat, Allah sarki muchan kauye, mushan kauye bawon Allah, ×2
Mai neman na abinci a kanchi komai kaji!
yeaah Bash nazo da tsokaci akan al ummar kasata, masu kallon mushan kyauye, kallon banza a kaskance.
Dan Allah kunzo kujini, ga bayani na kujini
Munbar gida da jiharmu muna aiki dan kasarmu
Maimakon ma a yabemu saidai kullum a zagemu, a zagemu a kushemu, wai an Raina kokarin mu,
Kaga muché bawon Allah yana aiki Babu lambah, ga iyaye ga iyali ga chekaru sun bigechi,
koma yadau dukk biyanchi a abinci ke kachechi, to hakan ma bai isarchi, ga bukatu dukk a kanchi, to fah wannan zaku duba kafin wuya ta kashemu,
Muchan kauye dan uwana
Lokaci yayi daya kamata mu tachi, tachi bana hankalibah, tachi bana hargitsi bah,
Sai mu tachi neman yanci, kalka zagi chugabanka, bana zagi ga chugaba bassssh,
aman kudai kudan dubah saiku karbi kudiirin mu,
ga tambaya jama'a ta,, ya kassata zata koma, bayan boko tana baya?
ya ilimi zai habaka muchan kauye baida gata!
Ga gaskiya kana ganta Babu damar ka fadeta, ga wakata na saketa!
Ga muryata saikuji ta, ga sakonku jama'a ta, kushe akan sana'ata chine farko a kasata, sa'ata rayuwa ta, bana barin mai tabata,
Muchan kauye in kun gane, Chine mai kula Yara, chizai gyara rayuwar su, Chine farko Chine tuche , Chine farkon tarbiyarsu,, kai mai wannan zaka kuche
Kai Barma baton girmamaka, halma takai dalibinka yana neman rayuwalka,.
kana kallo yama hauka,, Babu yancin kadau doka, droit de l'homme ta haneka,
Ya ilimi zai habaka kana tsoran dalibinka?
Al'ummar birni da kauye kuma dole saikun Farka, nace dole saikun kama, wannan sakon na kowa ne,
Wannan kichin kassata ne, kichin kasa saï dan kasa, baaaash nima dan kasa ne!
To yazamuyi su gane?...
zamani na lokaci na ga sakonku gomnatina al'umma na, masoyana, nasan kujin tausayi na
kuttayani aika sako,, sako zuwaga gomnati na, bash naku Muchan kauye, mushan kauye bawon Allah,
Mai neman na abinci akanchi komai kaji
Manyan mu ku dubah Allah, kuba muché karfin gwiwa, saiku duba yanayin mu, saiku dubah maganar mu, saiku gaira sana'ar mu
Dukkda kunsan rayuwarmu bamuyinta a garin mu, numa yawo cikin daji, ko'ina ma sai'akaimu,
bah munce bah a lelemu a goya mu mudai sauyi muke nema,
sana'ar mu muga sauyi, akan aikin da mukeyi kalilan ne ke yaban mu, ko munyima ba'a gani balle zancan a yabamun,
Muna aiki Babu fachi, ga albachin bai isarmu, mudai kullum cikin bachi, raywarmu babu dadi,
Saidai Manya masu bureau sune kadai kejin dadi suji A.C suci kaji, mota A.C, gida A.C, shan ruwama saina faro🍷
Kassh, Abun hauchin da takaici muchan kauye rayuwarchi, chidai kullum cikin daji.